1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harris ta samu goyon bayan 'yan Democrat

July 23, 2024

Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris za ta fara yakin neman zaben shugaban kasa a karon farko a wannan Talata a jihar Wisconsin mai matukar muhimmanci.

Hoto: picture alliance/dpa

Kokarin fara yakin neman zaben ya biyo bayan alkawarin da wakilan masu zabe na jam'iyyarta ta Democratsuka yi mata cewa ita za su zaba a matsayin 'yar takarar shugaban kasa ta jam'iyyar a makonni masu zuwa.

Harris ta zama wadda ake kyautata zaton za ta samu takarar jam'iyyar Democrat ne bayan da Shugaba Joe Biden ya janye aniyarsa ta takara a ranar Lahadi tare da nuna goyon bayansa a gare ta bayan makonni da aka kwashe ana tabka rikicin cikin gida a jam'iyyar kan fitar da dan takarar da ke da karfin tunkarar madugun adawa na jam'iyyar Republican, Donald Trump.

A ranar Litinin da daddare, Kamala Harris, a cikin wata sanarwa ta ce ta yi farin cikin yadda a kasa da sa'o'i 36 ta samu goyon bayan wakilan masu zabe na jam'iyyar domin ta zama 'yar takarar shugaban kasa, tana mai nuna shaukin karbar wannan nauyi da 'yan jam'iyyar suka dora mata.

Wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya gudanar ta nuna yadda Harris ta samu goyon bayan 'delegate' wato wakilan masu zabe 2,500 sabanin 1,760 da take bukata domin samun takarar. Duk da cewa 'delegate' din za su iya sauya matsayarsu kafin ranar zabe, amma tarihi ya nuna ba a taba samun wanda ya samu yawan kuri'u haka a irin wannan kuri'a ta jin ra'ayin jama'a ba.