1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hasarar rayuka a faɗan sojojin Burkina Faso

June 4, 2011

Taho mu gama tsakani sojojin Burkina faso da ke bore da kuma takwarorinsu na gwamnati ya haddasa mutuwar mutane bakwai ciki har da farar hula ɗaya a birnin Bobo Dioulasso.

Sojojin ƙasar Burkina FasoHoto: AP

Gwamantin Burkina Faso ta bayyana cewar mutane bakwai ne suka rasa rayukansu ciki har da mace guda a lokacin da aka fafata tsakanin sojojin da ke bore da kuma waɗanda ke biyeyya ga shugaba Compaore a birnin Bobo Dioulasso da ke zama cibiyar cinikayyar ƙasar. Ministan wannan ƙasa da ke kula da al'amuran cikin gida da kuma na tsaro wato Jerôme Bougouma ya nunar da cewar ɗaukacin dakaru shidan sun rasa rayukansu ne a cikin barikan sojoji, yayin da ita kuma matashiyar harsashi ya ritsa da ita a daura da inda ake taho mu gaman.

Fararen hula 25 da kuma sojoji takwas ne suka ji raunuka tun bayan da gwamnati ta ɗauki matakin murƙushe boren sojoji da ya ki ci ya ki cinyewa. Tun dai wasu makwanni da suka gabata ne dai jami'an tsaro ke tayar da ƙayar baya akai akai, tare da kwasar ganima a shagunan 'yan kasuwa da nufin neman tilastawa gwamnati biyansu albashi da kuma alawuns da suke binta. Bayan ma dai sojoji da kuma 'yan sanda, su ma dai ɗalibai sun shafe makwani suna maimata zanga-zangar domin tilastawa gwamnati inganta mummunan halin rayuwar da suke ciki.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal