1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nazari kan zaben 'yan majalisar dokoki a Iran

Usman Shehu Usman GAT
February 20, 2020

Masu hasashen kan siyasar kasar Iran, na cewa akwai alamar a samu karancin masu fitowa a zaben majalisar dokokin da zai gudana a wannan Jumma'a, zaben da masu neman sauyi ke sa ran samun sakamako mai kyau.

Iran Wahlen l Wahlurnen
Hoto: FARS

Masu hasashen kan siyasar kasar Iran, na cewa akwai alamar a samu karancin masu fitowa a zaben majalisar dokokin da zai gudana a wannan Jumma'a. Akwai dai masu bukatar sauyi da dama, amma kuma bisa yadda aka gani tun shekarun da suka gabata, zababbun suna da rauni wajen iya kawo sauyi a Jamhuriyar Musuluncin. 

Kasar Iran na da mutane miliyan 58 da suka isa kada kuri'a, amma ana kyautata zaton cewa za a samu karancin masu fitowar kada kuri'a ba don komai ba sai yananyin da kasar ta fada a yanzu. Wani binciken da wata cibiya a jami'ar Tehran ta gudnanar ya nuna akawai alamar cewa wasu daga cikin unguwannan Tehran babban birnin kasar ko fitowar zabe ba za su yi ba. A zaben 'yan majalisar dokokin shekara 2016 kashi 50 cikin dari ne suka fito zabe a fadin kasar, kuma ga al'ada akan samu fitowar masu zabe kashin 62 cikin dari. Mohammad Sadeq Dschawadi Hesar, da ke zama mamba a jam'iyar neman kawo sauyi yanan daga cikin wadanda ba za su fito zaben ba:

Hoto: Getty Images/AFP/B. Mehri

"Ginshikin zaben dai a kullum na kasancewar matasa ne da dalibai da 'yan boko, to amma bisa ga dukkan alamu a yanzu sun gaji da alkawuran da ba'a cikawa, suna ciki da fushi. Musamman kasancewar ba su ga mafita ba bisa rikicin da kasar ta fada tun shekaru biyu da suka gabata"

Amma zaben 2016, ya tabbatar da karya karfin masu neman sauyin fiye da yadda suka zata. Ko da shike idan aka yi la'akari da matsin tattalin arziki da kasar ke fuskanta a yanzu, hakan na kara sa jama'a fusata kan hukumomin, abin da ya jawo zanga-zanga a wasu biranen kasar, bayan da ba zato hukumomi suka rage tallafin da suke bai wa makamashi. To sai dai jami'an tsaron sun yi amfani da karfi wajen murkushe boren da aka yi wa gwamnati. Sadegh Zibakalam masanin siyasa ne, wanda ya yi tsokaci kan zaben na Iran: 

"Mutanen na ganin cewa kusan duk wadanda ake zaban basa iya aiki da ra'ayoyinsu, walau 'yan majalisa ko shugaban kasa. Kusan dukkan mahimman abubuwa daga sama ake turo masu. Don haka akasarin masu zabe na aza ayar tambaya shin mene ne ma dalilin yin zaben? Mafiyawan irin masu wannan ra'ayin sune ke kokarin neman an kawo sauyi a tsarin siyasar kasar. To amma akwai fa mutanen da ko da yaushe ke sh'awar tsarin siyasar kasar da ake amfani da shi yanzu, kuma a kullum suna zuwa zabe, musamman suna zaban 'yan takaran da ke da ra'ayin mazan jiya"

Hoto: ISNA


A yanzu babbar matsalar da ke gaban hukumomin kasar Iran ita ce batun kahon zukar da shugaban Amirka Donald Trump ya saka wa kasar, inda Trump ya bayyanan cewa takunkumi mai tsananin da ya saka wa kasar ya sa an fara yi wa gwamnatin bore, abin da yake fatan zai iya kawo karshen mahukunta da ke hana ruwa gudu a kasar. To sai dai wannan manufar ta Amirka da wuya ta cimma nasara, kamar yadda aka ga Iraniya sun zama tsintsiya a lokacin da aka kashe Janar Soleimani. A kasar ta Iran dai zaban majalisar dokokin bana, akwai 'yan takara kimanin 9000, wadanda ke takara, don zama a majalisar dokoki mai kujeru 290.