Hasashen asusun IMF akan tattalin arzikin duniya
April 14, 2005A shekarar da ta gabata tattalin arzikin duniya ya samu bunkasa ta kashi 5%, wacce ta kasance mafi girma a cikin shekaru goma da suka wuce. Amma a halin da muke ciki yanzu an samu dan koma-baya ga wannan bunkasa. Dangane da wannan shekarar da muke ciki kuwa, asusun ba da lamuni na IMF yayi hasashen samun bunkasa ta kashi 4.3%, ko da yake za a ci gaba da samun gibi dangane da bunkasar a tsakanin sassa dabam-dabam na duniya. An saurara daga jami’in asusun na IMF Raghuram Rajan yana mai bayani game da haka, inda yake cewar:
Bunkasar ta dogara ne kacokam akan ci gaban tattalin arzikin Amurka da kuma fadi tashin da ake samu a kasuwannin kasashen Asiya, a yayinda a daya bangaren kuma ake ci gaba da fama da tafiyar hawainiya a kokarin ta da komadar tattalin arzikin kasashen Turai dake amfani da takardun kudin Euro.
A yayinda hasashen na AMF ya nuna cewar a wannan shekarar da kuma shekara mai zuwa kasar Amurka zata samu bunkasar kashi 3,6% ga tattalin arzikinta, kasashen Turai masu amfani da takardun kudin Euro duka-duka bunkasar tattalin arzikinsu ba zata bzarce kashi 1, 6% ba. Jamus ce zata fi jin radadin wannan tafiyar hawainiyar, inda bunkasar tattalin arzikinta zata tuke akan kashi 0,8%. Musabbabin haka, kamar yadda Raghuram Rajan ya kara da bayani shi ne tsumulmular kudaden da jama’a ke kashewa a nahiyar Turai, a yayinda a can Amurka, mutane ba sa ba da la’akari da wata manufa ta ajiya. Amma babbar barazanar da ka iya zama cikas ga bunkasar tattalin arzikin duniyar a wannan shekara ita ce hauhawar farashin man fetur. Kamar yadda aka saba, a wannan karon ma a cikin rahotonsa na rabin shekara asusun IMF yayi kakkausan suka akan gibin kasafin kudin da Amurka ke fama da shi, sannan yayi kira ga kasashe masu matsakaicin ci gaban masana’antu, kamar dai Indiya, da su dauki nagartattun matakai na kyautata handoyin sadarwarsu, sannan ita kuma China ta daidaita darajar takardun kudinta. Kazalika asusun na IMF yayi kira ga kasashen Turai da su aiwatar da garambawul ga manufofinsu na kyautata jin dadin rayuwar jama’a.