Gommai sun mutu a hatsarin jirgi a Indiya
June 2, 2023![Train accident in Balasore, India](https://static.dw.com/image/65811836_800.webp)
Shaidun gani da ido da jami'ai sun shaidawa kafafen yada labarai na cikin gida cewa, jirgin fasinja na Coromandel Express da wani jirgin dakon kaya sun yi karo a kusa da Balasore mai tazarar kilomita 200 daga Bhubaneswar babban birnin jihar.
Kazalika hatsarin ya kuma ritsa da wani jirgin fasinja na biyu, a cewar babban sakataren Odisha Pradeep Jena, amma har yanzu ba a fayyace yadda lamarin ya kasance ba.
Sai dai wasu jami'ai da ba a bayyana sunayensu ba sun ce kimanin mutane 50 ne ake fargabar sun mutu, a yayin da wasu fasinjoji da yawa ke makale a karkashin jirgin dakon kayan.
Ofishin mataimakin sufeto janar na ‘yan sandan Balasore ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa akalla mutane 200 ne sun jikkata, kuma yawancinsu munanan raunuka.