Hatsarin Jirgin ƙasa a Indiya
July 19, 2010Sama da mutane 50 suka rasa rayukansu a wani haɗarin layin dogo da ya auku a Gabacin ƙasar Indiya.
Wani jirgin ƙasar wanda yake kan hanyasa ta zuwa Calcuta hed kwatar Bengale, ya ci karo da wani jirgin dake a tsaye a wata tashar ta Birbhum inda ya dake shi ta baya,
abinda ya yi sanadiyar cirewar taragon baki ɗaya wanda galibi jamaar da lamarin ya rutsa da su a ciki ,suke.
Da ya ke magana da manema labarai wani jam'in 'yan sanda na yanki ya shaida cewa haryanzu suna kokarin cire gawarwaƙin jama'ar daga cikin tarkaccen jirgin, sanan ya ce ba mamaki na gaba addadin mutane da suka mutu a hatsarin ya ƙaru.
Wannan dai shine hatsarin jirgin ƙasar na biyu da aka samu a yankin na Bengale, bayan wanda ya faru watannin biyu da su wuce wanda a cikinsa mutane 150 suka mutu wanda kuma aka ɗaura alhaƙinsa akan yan tawaye na Maoist.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar