Hatsarin jirgin ruwan 'yan gudun hijira
July 16, 2015Jami'an kan teku a Turkiyya sun ce a kwanaki biyar din da suka gabata sun ceto 'yan gudun hijira fiye da dubu daya da dari uku wadanda ke kan hanyarsu ta zuwa Girka. Shidda daga cikinsu wadanda 'yan asaslin Siriya ne sun nitse, bayan da jirgin ruwan da suke ciki ya kife kusa da tsibirin Lesbos da ke Girkar.
Kafofin yada labaran Turkiyya sun rawaito cewa, tun daga farkon wannan shekarar, 'yan gudun hijira fiye da dubu 14, -yawancinsu 'yan Siriya- mahukuntan Turkiyya suka ceto daga kan ruwan, adadin da ya ninka abin da aka samu a bara kadai.
Ko a ranar laraba, jami'an kan tekun Italiya sun ce sun ceto wasu mutane 2700, tare da tallafin jirgin ruwan Jamus da kungiyar agajin Medecins sans Frontieres.
A wannan shekarar kawai ana kiyasin cewa 'yan gudun hijira dubu 150 sun riga sun isa Turai ta kan Tekun.