1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hauhawar Farashin mai

January 3, 2008

Rahotanni daga ƙasar Amurka sun ce farashin ɗanyen mai ya haura zuwa dala 100 kan kowace ganga. ‚Yan kasuwar man a New York sun ɗora alhakin ƙaruwar farashin ne kan ci gaba da tashe tashen hankula a wasu ƙasashe biyu membobin Ƙungiyar Ƙasashe masu arzikin man fetur OPEC wato Najeriya da Aljeriya tare kuma da faɗuwar darajar takardar kuɗin dala.