1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSaudiyya

Musulmi miliyan daya da rabi na yin tsayuwar Arfa

June 5, 2025

An gudanar da hudubar Arfa a Saudiyya inda mahajjata suka taru daga kasashen dabam-dabam na fadin duniya, an fasara hudubar zuwa wasu harsuna ciki har da na Nigeriya.

Saudi-Arabien Arafat | Muslime beten bei Hajj-Pilgerfahrt
Hoto: Rafiq Maqbool/AP/picture alliance

Daruruwan mutane sun yi cicirindon hawan dutsen Arfa wurin da Annabi Muhammad tsira da aminci su tabbata a gare shi ya yi huduban sa na karshe. Hawan Arfa na a matsayin kololuwar aikin Hajji ga alhazai

Shekh Sale Bin Abdullah daya daga cikin limaman Masallaci Makka ya gudanar da hudubar ke nan cikin harshen Larabci inda aka fara yin fasara zuwa harsuna 34 ciki har da Hausa da Yoruba da Fulatanci.

Hoto: Amr Nabil/AP Photo/picture alliance

Sai dai wasu  harsunan an yi fasarar rubutu wasu kuma ta murya harsunan na Nigeriya an fasara su ta hanyar rubutu. Kuma hudubar ta kunshi kara Imani da Allah da bauta masa shi kadai gami da jaddada mahimmancin tauhid ga Allah da kuma bin duk abin da manzonsa ya zo da shi.

Hoto: Amr Nabil/AP/picture alliance

Malam Bello na daya daga cikin malaman  Nigeriya  da suka halarci aikin Hajj ya bayyana cewar tsarin yin fasarar ya yi kyau sosai.