Hayaƙi ya turnuƙe birnin Maiduguri
July 23, 2011An samu tashin Bam a birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno mai fama da hare-hare, harin na yau an kai shi en a wata unguwa mai suna Budum dake kusa da gidan mai martaba Shehun Borno. Wannan harin ya yi kama da wanda ‘yan kungiyar ta Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati Wal Jihad da aka fi sani da suna Boko Haram ke kaiwa. Har ya zuwa yanzu dai ba'a tabbatar da irin hasara rai ko dukiya a sanadiyyar wannan fashewar ba, sai dai mazauna Anguwar da waklin mu Al-Amin ya tuntuba ta wayar tarho, sun shaida masa cewa, sun ji karar fashewar daga baya kuma hayaki ya turnuke sararin samaniya garin, daga nan kuma sai jama'a suka fara gudu don tsira da rayukan su. Jami'an tsaro dai sun killace duk hanyoyin shiga Anguwar tare da yin binciken kwakwab.
Mawallafi: Mouhamad Awal Balarabe
Edita: Usman Shehu Usman