Najeriya Matashiya mai sana'ar kiwon kifi
December 16, 2020Matashiyar Sakina Tijjani, wadda tun bayan kammala aikin bautar kasa ta yi watsi da aikin gwamnati da na wani kampani sakamakon karamin albashin da ake biyan ta, ta yi tunanin neman yin dogoro da kai inda ta rungumi kiwon kifi a cikin harabar gidan su ta yadda take kula da dawainiyar ta dama ta sauran 'yan uwa. Babu shakka dai akwai nasarorin da ta samu, wadanda suka hada da daukar nauyin ci-gaba da karatun ta na digirin digirgir,da kuma yadda sana’ar ke tallafa wa Sakina wajan kulawa da iyayen ta. Duk da irin ci-gaba da ta samu, harwa yau dai akwai manyan kalubalen da ke ci mata tuwo a kwarya wajan bunkasa sana'ar. Babban kalubalen da sana’ar ke fama da ita, shi ne na karancin ruwa da rashin isassun kudade da tsadar kayayyakin abincin kifi.