HdM: Mai na'urar ba wa fanka caji
April 27, 2022Shi dai Muhammad Mai Anini matashi ne da ya kirkiri na'urar dake baiwa fanka caji ta yadda ko babu wutar lantarki za ta iya aiki na tsawon wasu sa'o'i. Muhammad Mai Anini ya kirkiri na'urar cajin fankar ne a daidai lokaci da ake fama da tsananin zafi da karancin wutar lantarki a Kano da sauran wasu jihohin arewacin Najeriya.
"Mutun ne zai sayi sabuwar fanka ba za ta wuce sa'a biyu ba sai ta dauke, daga nan ne na soma wani bincike game da yadda za a kara tsawon lokacin da fanka za ta dauka, na kuma yi nasara da hada wannan fasaha za a iya yin sa'o'i 24."
A cewar matashi Muhammad Mai Anini, kirkiro wannan fasahar da ya yi a daidai lokacin tsananin zafi da ake fama da shi, ga karancin wutar lantarki, na daga muhimman nasarorin da ya samu a rayuwa.
"Mutun zai kawo fanka idan yaga ta kwana tana aiki, sanadiyar jin dadin aikin da muka masa, sai ya dinga yi wa mahaifana addu'a, wannan na sa ina jin dadi da farin ciki, kuma yana bani kwarin gwiwar ci gaba da nazari, cikin ikon Allah kuma muna samun ci gaba kullum, idan na hada a yau gobe kuma sai a samu wasu sabin fasahohi."
Duk da haka matashi Muhammad Mai Anini ya bayyana cewa yana fuskantar wasu kalubale da ke ci masa tuwo a kwarya ciki har da na saba alkawari da masu kawo aiki ke yi masa. Misali mutun zai kawo fanka yace a gyara masa, sai an wahala an siyo kayan gyaran daga baya idan ka bashi zai ce maka a gobe zai kawo kudin, ko sai an kammala hadawa baki daya, ya kasa zuwa karba."
Ita sana'ar dogaro da kai babban jari ne da baya karewa a wajen matashi mai hangen nesa irinsu Muhammad Mai Anini.