HDM: Matasa maza masu 'yan makaranta masu sana'ar tuya
December 4, 2019Saleem Ahmed Ishaq da Ahmad Yakubu matasa ne 'yan makaranta da ke neman na kansu a Kano, wadanda suka rungumi sana'ar tuya da ba kasafai ake ganin maza na yi ba a tsakanin al'umma, musamman matasa wadanda suka yi karatu.
Ahmad Yakubu, ya bayyana irin sana'ar da shi da 'yan uwansa ke yi a unguwar Tukuntawa da ke jihar Kano. Akwai sana'u da yawa da yawa da ba kasafai ake ganin maza na yinsu ba. Tuyar Kosai da awara da ma koko a bakin titi sana'a ce da aka jima da sanin mata na yi. Sai dai sabanin haka Saleem da dan uwansa Ahmad da kannensu maza guda biyu sun rungumi wannan sana'a ta tuya a bakin titi safe da yamma, wanda a cewarsu sun rungumeta ne saboda yanayi na rayuwa da neman abun dogaro da kai, kasancewar sun taso suna kallon mahaifiyarsu na yi, kuma kasuwa sai dai hamdala a cewar Ahmad.
Tun daga matakin firamare har sakandare zuwa gaba da sakandare a yanzu, wadannan matasan na ci-gaba da cin gajiyar wannan sana'a, kuma akwai karin nasarori a cewar Saleem Ahmed Ishaq.
Sai dai kamar ko wace sana'a wadan nan matasa su ma na fuskantar kalubale musamman a matsayinsu na samari, 'yan makarantar gaba da sakandare masu tuya a bakin titi, kamar yadda Ahmed ya bayyana. Saleem da Ahmad sun bada shawara ga sauran matasa. Ganin wadannan matasa suna sana'arsu na da ban sha'awa kuma a cewar Saleem yana da dumbin buri a rayuwarsa.