1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Katsina: Matashiya mai sana'ar cake

September 16, 2020

Wata matashiya a jihar Katsina Safiya Lawal Musa da ta kammala karatun jami'a, ta kama sana'ar yin cake a gidan mijinta domin dogaro da kanta. Matashiyar tace tana samun ciniki daga al'umma a jihar.

Nigeria Kuchen Bäckerin
Safiya Lawal Musa matashiya mai sana'ar cake a Katsinan NajeriyaHoto: DW/Y. I. Jargaba

Matashiyar ta ce wannan sana'a na taimaka mata wajen gudanar da hidindumun yau da kullum ba sai ta jira mai gidanta ba, wanda acewarta da ma hakan shi ne makasudin kama sana'ar bayan kammala jami'a.

Sai dai matashiyar ta ce duk da nasarorin da ta samu a wannan sana'a, to akwai kalubalen da take fuskanta musamman da abokan hulda. 

Sakamakon jin dadin wannan sana'a ta cake da da take yi dai, matashiya Safiya ta nusar da 'yan uwanta da su tashi tsaye su kama sana'a. Yakubu Lawal shi ne mijin matashiyar, ya kuma ce shi kansa yana amfana da wannan sana'a da matarsa ke yi.