1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Amfani da kwali wajen yin fulawa

Gazali Abdou Tasawa LMJ
September 8, 2021

A Jamhuriyar Nijar wata matashiya mai suna Roukayyatou Karimou Moumouni da ta kammala karatunta a fannin aikin likita, ta rungumi sana'ar sarrafa kwalaye da takardu zuwa kayan adon daki ko ofisoshi.

DW Reportage | Niamey Möbel Recyclen+
Hoto: Gazali Abdou Tasawa/DW

Matashiyar dai, ta rungumi wannan sana'a domin samun kudin kashewa da taimakon iyayenta. Takan kuma horas da matasa da dama wannan fasaha tata ta sarrafa kwalaye zuwa kayan ado da kuma ke zama wata hanya ta tsaftace muhalli. Rakiyatou Karimou Moumouni bayan kammala karatun nata ta fara aiki. Sai dai kuma Allah ya yi mata baiwa ta iya sarrafa kwalaye da takardu wadanda wasu lokuta take tsintowa a bola.

Hoto: Gazali Abdou Tasawa/DW

Tana dai mayar da kwalaye da takardun kayayyakin ado iri-iri ne na kawata daki ko ofis da suka hadar da kujeru da tebura da fulawa. Akasari dai matan aure ne ke sayen kayyakin adon dakin da take tallatawa a shafukan sada zumunta, sana'ar da ta ce na samar mata da kudin shiga. Matasa da yara masu yawa ne dai Roukayyatou ke horas wa a fannin sarrafa kwalayen zuwa kayan ado, kuma a yanzu haka ta fara gina wani shago a cikin gidansu inda za ta rinka baje kolin kayan adon da take sarrafawa daga kwali da kuma horas da yaran unguwa.