1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mace mai sana'ar kuli-kuli Katsina

April 29, 2020

Wata matashiya a jihar Katsina da ta kammala karatun sakandire babu halin ci gaba da karatun, ta kama sana'ar sayar da kuli-kuli a bakin titi domin dogaro da kai da taimakawa iyayenta.

DW Beitrag Nigeria | Katsina Erdnussöl
Matshiya Hauwa'u mai sana'ar kuli-kuli a Katsina NajeriyaHoto: DW/Y. Ibrahim Jargaba

Matashiyar mai suna Hauwa'u Lawal dai na zama a bakin tashar kofar Marusa cikin birnin Katsina, inda take sayar da kuli-kulin, kuma ta ce gajiya ta yi da takurawa iyayenta da bani-bani ta saukaka musu ta kama wannan sana'ar. Akwai tarin kalubale da wannan matshiya ta ce ta fuskanta a baya a wannan sana'ar, amma kuma bai sanyaya mata gwiwa ba, a cewarta juriyar da ta yi ce ta sanya har aka samu mafita, sai dai har yanzu akwai kalubalen da ba a rasa ba.

Matashiya Hauwa'u dai ta bayyana cewa ta kammala karatunta na sakandire kuma tana da fatan ci gaba da karatun, amma duk da haka ta ga babu abin da ya kamace ta illa ta zamo mai dogaro dai kanata. A kasar Hausa akwai al'adar raina sana'a musamman tsakanin matasa, abin da ya sanya Hajiya Yalwati Bature Abdullahi ta shawarci Hauwa'u da ta kawar da kanta daga masu irin wannan dabi'ar.

Sakamakon yadda wannan matashiya Hauwa'u ta kama wannan sana'a domin tsira da mutunci ya sanya ta zama abar kwatance a cikin kawaye kuma abar alfahari ga iyayenta saboda irin gudummuwar da take ba su.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani
Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW

Karin labarai daga DW