1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiAfirka

Matasiyar da ta kware sakar kayan sanyi

November 3, 2021

Matashiya Fatsuma Haruna da ke da zama a Gombe da ke Najeriya ta zabi sana'ar saka kayan sanyi na yara da manya bayan kammala karatunta, inda ta bude masana'anta tare da daukar wasu aiki da ma koyawa wasu.

Nigeria Gombe HdM | Stickereien
Hoto: Al-Amin Suleiman Mohammad/DW

Ita dai matashiya Fatsuma Haruna wacce take yin sakar da hannun ta maimakon amfani da na'urorin zamani inda ta ce tana alfahari da sana'ar saboda ta faro ta da jimawa. A cewar ta zabi yin wanann sana'a ne maimakon jiran aikin gwamnati saboda ribar da take samu kuma saboda za ta ba ta damar ita ma ta dauki wasu aiki ta koya musu har su dogara da kansu.

Sau da yawa ana ganin salon sana'ar saka da Malama Fatsuma take yi wato na yi da hannu kamar ya zama tsohon yayi saboda yadda aka ci gaba ake yi da na'urori. Sai dai a wajen ta bai zama tsohon ya yi ba saboda yadda ta lakanci yin sakar da hannu kuma ta na yi da yawa ta sayar a kan lokaci.

Babbar shawarar da Fatsuma Haruna ta bai wa matasa musamman ma mata ita ce su rungumi sana'ar hannu ko ya take saboda masu yin ta ba rasa kudin kashewa har ma da na biyan bukatun yau da kullum.