1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Henry Kissinger ya mutu yana da shekaru 100

November 30, 2023

Kasashen duniya na jimamin mutuwar tsohon babban jami'in diflomasiyyan Amurka Henry Kissinger wanda ya mutu a ranar Laraba 29.11.2023 yana da shekaru 100.

Henry Kissinger
Henry Kissinger ya mutu yana da shekaru 100Hoto: Brendan Smialowski/AFP

A lakacin da yake raye marigayi Henry Kissinger ya rike matsayin sakataren harkokin wajen Amurka a lokacin yakin cacar baka karkashin gwamnatocin Richard Nixon da Gerald Ford tsakanin shekarun 1972 i zuwa 1975.

Shi dai Kassinger dan asalin kasar Jamus ne kuma an haifasa a shekarar 1923 a Bavaria, sai dai ya dauki takardun Amurka bayan ya yi gudun hijira kasar a lokacin da yake da shekaru 20 da haihuwa.

Babbar rawar da ya taka a fagen diflomasiyya a duniya ita ce daidaita tsakanin Rasha da China a shekarun 1970, sai dai kuma juyin mulkin da Amurka ta kitsa a kasar Chile a shekarar 1973 da mamayar Timor ta Arewa a shekarar 1975 da kuma yakin Vietnam sun daudada tasirinsa a idon duniya. To amma bajimtar da ya nuna wajen sasanta rikice-rikice ciki har da jagorantar yarjejeniyar tsagaita buda wuta a Vietnan sun farfado da tauraronsa, lamarin da ya kai shi ga lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel a shekarar 1973 wacce ta haifar da cece-kuce. 

Henry Kissinger ya cika shekaru 100 a duniya a watan Mayun da ya gabata kuma ziyarsa ta karshe ita ce wadda ya kai kasar China a watan Yulin da ya gabata inda ya gana da shugaba Xi Jinping.

Kasashen duniya na ci gaba da bayyani alhini a game rasuwar tsohon jami'in diflamasiyyan wanda ya taka muhinmiyar rawa a siyasar Amurka da kuma hulda tsakanin kasa da kasa.