1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila na gargadin 'yan Lebanon

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 15, 2023

A karon farko tun bayan barkewar rikici tsakanin Isra'ila da mayakan Hamas, jiragen yakin Isra'ila sun jefa takardun gargadi ga fararen hula a yankin Kudancin Lebanon.

Isra'ila | Kan Iyaka | Lebanon | Rikici | Hamas | Zirin Gaza | Falasdinu
An jibge tankokin yaki da kuma makaman Isra'ila a kan iyakarta da LebanonHoto: Lisi Niesner/REUTERS

Takardun dai na gargadin fararen hular da kada su bayar da kariya ga mayakan kungiyar Hezbollah, suna mai bayyana su a matsayin gagarumar barazana da ka iya cutar da su. Jami'an tsaron Lebanon din dai sun bayyana cewa, an jefa takardun a wurare da dama da ke kan iyakar kasar da Isra'ila. Tun bayn da kungiyar Hamas da ke gwagwarmaya da makamai a yankin Zirin Gaza na Falasdinu ta kai harin ba-zata a Isra'ila a ranar bakwai ga watan Oktobar wannan shekara da muke ciki ne dai, ake samun musayar wuta tsakanin mayaka masu dauke da makamai kamar Hezbollah a bangaren kan iyakar Isra'ila da Lebanon din a hannu guda kuma da sojojin Isra'ilan a kan iyakokinsu.