1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hezbollah ta gargadi Lebanon kan sulhu da Isra'ila

Abdul-raheem Hassan
March 25, 2026

Shugaban kungiyar Hezbollah Naim Qassem yace shiga yarjejeniya da Isra'ila ana tsaka da luguden wuta zai tilasta wa Lebanon mika wuya, ya kuma bukaci gwamnati da ta janye matakin kwance mata damarar yaki.

Shugaban Hezbollah, Naim Qassem
Shugaban Hezbollah, Naim QassemHoto: Houssam Shbaro/Anadolu/picture alliance

A wani jawabin da aka karanta ta talabijin a madadinsa, Qassem ya yi kira ga al'ummar Lebanon da su rungumi "hadin kan kasa", yana mai cewa za a iya cimma hakan idan gwamnati ta janye matakin da ta dauka a ranar 2 ga watan Maris na haramta ayyukan soji na kungiyar.

Yanzu haka dai yakin Lebanon ya yi sanadiyyar mutuwar ma'aikatan jinya 42 tun farkon watan Maris a daidai lokacin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare.

A wani lamari na baya-bayan nan, wasu ma’aikatan jinya biyu sun rasa rayukansu a lokacin da aka taka babur din su a lokacin da suke bakin aiki. Sojojin Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a kasar Labanon a daidai lokacin da Amurka da Isra'ila ke yakin Iran, inda suka kashe fiye da mutane 1,000 a cewar ma'aikatar lafiya ta Lebanon.

Tawagar likitocin da ke da alaka da kungiyar Hezbollah da ta Amal na daga cikin wadanda abin ya shafa, inda hukumomi suka ce ana ci gaba da luguden wuta kan masu aikin ceto.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana nazari kan lamarin, yayin da ta ci gaba da zargin kungiyar Hezbollah da amfani da motocin daukar marasa lafiya da kuma cibiyoyin kiwon lafiya wajen ayyukan soji. Sai dai jami'an kasar Labanon suna zargin Isra'ila da kai farmaki kan jami'an agaji da gangan, suna masu cewa hakan ya saba wa dokokin kasa da kasa.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW