1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hezbollah ta ce ta kai hari cikin isra'ila

November 24, 2024

Babban jami'in kula da harkokin waje na Kungiyar Tarayyar Turai, Josep Borrell ya yi kira da a gaggauta tsagaita bude wuta a rikicin Isra'ila da Hezbollah.

Libanon Beirut 2024 | Rettungskräfte durchsuchen nach israelischem Luftangriff nach Opfern
Hoto: Hassan Ammar/AP Photo/picture alliance

A lokacin da yake ganawa da shugban majalisar Lebanon, Nabih Berri da ke shiga tsakani a rikicin a madadin Hezbollah, babban jami'in kula da harkokin waje na Kungiyar Tarayyar Turai Josep Borrell ya ce hanyoyin samun mafita su ne amince wa da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma mutunta dokar kasa da kasa ta kwamkittin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

Kungiyar Hezbolla ta sanar da harba jirage marasa matuka da makamai masu linzami zuwa Isra'ila bayan da rundunar sojin Lebanon ta sanar da rasa sojinta daya a harin da Isra'ila ta kai kudancin kasar.

Karin bayani: Sabon shugaban Hezbollah ya ce zai ci gaba da yakar Isra'ila

Kungiyar da ke samun goyon bayan Iran ta bayyana cewa, a karon farko ta kaddamar da wani hari ta sama ta hanyar amfani da gungun jiragen sama marasa matuka, kan sansanin sojojin ruwa na Ashdod da ke kudancin Isra'ila. Isra'ila ba ta ce uffan ba kan harin, sai dai tun da fari ta ce an ji sautin gargadi na koma cikin gida a yankuna da dama a tsakiya da kuma arewacin kasar ciki har da babban birnin kasar Tel Aviv. Rundunar ta kuma ce ta kakkabo wasu kananan makamai 55 da aka harba arewacin Isra'ilar.