1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hezbollah ta ci alwashin ramuwar hari kan Israila

Abdullahi Tanko Bala
September 18, 2024

Hezbullah ta ci alwashin mayar da martani a kan Israila bayan fashewar daruruwan kananan na'urorin sadarwa da 'yan kungiyar ke amfani da su da suka tarwatse a Lebanon.

Libanon | Fashewar kananan na'urorin sadarwa
Hoto: Anwar Amro/AFP/Getty Images

Israila dai ba ta ce uffan ba a kan harin wanda ya hallaka mutane 12 ciki har da kananan yara biyu, yayin da wasu mutanen 2,800 suka sami raunuka.

Sai dai yan sa'oi bayan aukuwar harin, Israila ta ce za ta fadada yakin da Hamas ta haddasa a ranar 7 ga watan Oktoba, inda a yanzu za ta rika kai hari kan kungiyar Hizbullah

Shugaban Hizbullah Hassan Nasrallah ana sa ran zai yi jawabi a ranar Alhamis.