1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Hezbollah ta gargadi Lebanon kan tattaunawa da Isra'ila

May 12, 2026

Shugaban Hezbollah Naim Kassem ya bukaci gwamnatin Lebanon da ta kauracewa shiga tattaunawa ta kai tsaye da Isra'ila.

Hoto: Mohammed Zaatari/AP Photo/picture alliance

An dai shirya tattaunawar kwanaki biyu tsakanin Lebanon da Isra'ila a birnin Washington DC na Amurka, domin warware takaddamar da ke tsakanin kasashen na tsawon watanni biyu, tun bayan kirkirar kasar ta Isra'ila a 1948.

Karin bayani:Tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Lebanon ta fara aiki 

Kassem ya ce batun makaman da Hezbollah ta mallaka matsala ce ta cikin gida, kuma ba abu bane da ya kamata a tattauna shi a wajen taron Washington DC ba. Gwamnatin Lebanon dai ta bukaci kwance damarar makaman yakin Hezbollah, tun bayan ballewar yaki tsakanin mayakan kungiyar da dakarun sojin Isra'ila.

Karin bayani:Hezbollah ta ce sulhu da Isra'ila tamkar mika wuya ne 

Ministan lafiya na Lebanon Rakan Nassereddine ya shaida wa manema labarai cewa sun samu rahotannin mutuwar mutane 380, yayin da 1,122 suka samu raunuka tun bayan tsagaita bude wuta. Ya kara da cewa a jimlace mutane 2,882 tun bayan fara yakin, yayin da wasu mutanen kimanin dubu Tara suka samu raunuka.