Hezbollah ta kai hari a kan Isra'ila bayan tsagaita wuta
December 2, 2024Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta bayyana cewa ta kai farmaki kan wani sansanin sojin Isra'ila, a karon farko tun bayan da yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakaninsu ta fara aiki. A cikin wata sanarwa da ta fitar a birnin Beyrouth, kungiyar da ke samun goyon bayan Iran ta bayyana cewa ta kai hari kan tsaunin Kfar Chouba da Lebanon ke ikirarin cewa mallakinta ne amma Isra'ila ta mamaye.
Karin bayani: Hezbollah da Isra'ila sun cimma yarjejeniya
Sai dai sojojin Isra'ila sun yi ikirarin cewa Hezbollah sun harba makamai masu linzami guda biyu a sansaninsu. Saboda haka ne gwamnatin Isra'ila ta sha alwashin mayar da martani kan Hezbollah, a daidai lokacin da bangarorin biyu ke zargin juna da karya yarjejjeniyar tsagaita bude wuta. Kakakin majalisar dokokin Lebanon Nabih Berri ya yi ikirarin cewa Isra'ila ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta akalla sau 54 cikin mako guda. Sai dai fadar mulki ta Tel Aviv ta yi watsi da zargin keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta.