1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Hezbollah ta shirya wa Nasrallah jana'izar ban girma

February 2, 2025

Mai rikon mukamin shugabancin kungiyar Hezbollah ya ce za su gayyaci dukkan jagororin kungiyar da daukacin al'umma zuwa wajen jana'izar ban girman da za a gudanar a ranar 23 ga watan nan na Fabrairun nan da muke ciki.

Tsohon shugaban kungiyar Hezbollah Hassan Nasrallah
Tsohon shugaban kungiyar Hezbollah Hassan Nasrallah Hoto: Al Manar TV/AP/picture alliance

Kungiyar Hezbollah ta sanya ranar da za ta gudanar da jana'izar ban girma ta tsohon shugaban kungiyar Hassan Nasrallah, watanni biyar bayan da dakarun sojin Isra'ila suka halaka shi a yayin wani farmaki da suka bai kudancin birnin Beirut na kasar Lebanon.

Karin bayani: Isra'ila ta zargi Hezbollah da kaiwa MDD hari a Lebanon 

Sojojin Isra'ila sun kashe Nasrallah a ranar 27 ga watan Satumbar 2024, inda aka binne shi a asirce a wani kebantaccen wuri ba tare da an gudanar da babban taro ba.
 

 

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW