1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hillary Clinton ta yi kira ga Palestinu ta koma tebrin shawara

October 2, 2011

Sakatariyar harkokin wajen Amurika Hillary Clinton, ta bukaci Palestinu da Isra´ila su hau tebrin shawara domin girka kasashe biyu masu cikkaken 'yanci

Hoto: AP

Sakatariyar harkokin wajen Isara´ila Hillary Clinton ta yi kira ga Palestinawa su koma tebrin shawara da Isra´ila domin samun damar girka kasashe biyu masu cikkaken 'yanci ta hanyar tattanawa.

Clinton ,ta jaddada goyan bayan Amurika na tabbatar da Palestinu a matsayin kasa mai cikkaken 'yanci, amma fa ta hanyar shawara da Isra´ila sabanin matakin da shugaban Hukumar Palestinawa Mahmud Abbas ya dauka a Majalisar Dinkin Duniya.

A daya wajen, Hillary Clinton ta soki lamirin bani yahudu, wanda suka bayyana gina karin gidaje fiye da dubu a yankunan Palestinu.

Tuni dai Mahmud Abbas, ya ce ba zai sake komawa tebrin shawara ba,muddun Isra´ila ba ta daina mamayar yankunan Palestinun ba.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Usman Shehu Usman