Matashiya mai yin kayan makulashe
January 6, 2021Talla
Rukayya Abubakar Bajah matashiya ce da ke ajin karshe a jami'a, amma kuma ta rungumi sana'ar kayan makulashe, inda take yin gullisuwa da kwakumeti da carbin malam da makamantansu. Matashiyar dai ta rungumi sana'ar ne a wani mataki na kaucewa rashin aikin yi da kuma dogaro da kai.
A cewar matashiya Rukayya Bajah ta samu alkhairi mai yawa sakamakon sana'ar tata, kuma tana daukewa kanta kudin makaranta da sauran lalurorin yau da kullum, baya ga matasa da take koyawa sana'ar da kuma wadanda ke taimaka mata suke kuma cin abinci a karkashinta.