1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Matashi mai sana'ar yin turare a Kano

February 2, 2022

Wani matashi a jihar Kano da ke Tarayyar Najeriya, ya rungumi sana'ar harhada turare na Afirka da ma na Larabawa.

Faransa
Nau'in turarurruka da dama matashin ke yiHoto: Franz Chavaroche Nicematin/dpa/picture alliance

Matashin mai suna Malam Ibrahim wanda ake wa lakabi da Yellow, yana sana'ar yin turaren tare da sarrafa shi zuwa turarurrukan al'umomin yankuna da dama musamman yankunan Larabawa da na Afirka dabam-dabam. Matashin dai ya nakalci fasahar hada turarurrukan da su kan fitar da kamshi na musamman da babu irin sa. Koda yake matashin ya cimma nasarori masu tarin yawa a sana'ar tasa, ya bayyana cewa akwai tarin kalubale da yake fuskanta. A cewarsa sana'a ce a sai an jure, kasancewa a wasu lokutan har ciwuka ya kan ji sakamkon sarrafa itacen turare ko kuma amfani da kwalaben da yake dura turarurrukan. Sai dai duk da hakan ya nunar da cewa akwai bukatar matasa su jajirce su tashi tsaye domin su tsaya da kafafuwansu, maimakon jiran aikin gwamnati ko na kamfani da awsu lokutan ke haifar da zaman kashe wando sakamkon jiran gawon shanu na samun aikin yi da matsan kan yi.