1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashiya mai dinkin hula a Borno

September 9, 2020

Fauziyya Adamu Kida wata matashiya da ta shahara wajen koyar da mata da 'yan mata har ma da samari sana'ar dinkin hula, inda da yawa su ka iya san'ar tare da samun dogaro da kansu.

Nigeria Maiduguri | Coronavirus | Mützen & Social Distancing
Matashiya Fauziyya Adamu Kida mai sana'ar dinkin hula a jihar Bornon NajeriyaHoto: DW/A.A. Suleiman Muhammad

Sana'ar dinkin hula na daga cikin sana'o'i da suka yi fice tsakanin al'ummar jihar Borno, inda maza da mata manya da yara har ma da tsofaffi ke yin wanan sana'ar da wasu ke kallon ta a matsayin sana'ar gado. Sai dai ba kasafai ake samun masu ware lokaci suna koyawa wadansu ba musamman ma matasa, duk da cewa kuma akwai masu sha'awar koyar sana'ar domin samun abin dogaro da kai.

HdM: Manhajar Northfilx domin fina-finai

Bisa wannan ne matashiya Fauziyya Adamu Kida wacce kwararriya ce a dinkin hula da wasu sana'o'in hannun, ta kudiri aniyar koyawa matasa musamman 'yan mata sana'ar dinkin hular domin huta takaicin rayuwa. Ita dai Fauziyya ba ta karbar kudi wajen koyar da wannan sana'a, da ta dogara da ita wajen biyan bukatunta ciki har da kudin makaranta, a kokarin kara samun ilimi mai zurfi.
Wasu daga cikin 'yan mata da wakilin na DW ya tarar tana koyawa dinkin hular, sun bayyana min jin dadin su da kuma alfahari da abin da su ka koya. Fauziyya ta shaidawa wakilin DW cewa, ta samu nasarori da dama, koda yake ba a rasa kalubale, ammam hakan bai taba sawa ta yi kasa a gwiwa ba, inda ta ce tana matukar alfahari da koyar da matasa wannan sana'a.

Matasa da dama musamman ma mata, na koyon dinkin hula a wajen FauziyyaHoto: DW/A.A. Suleiman Muhammad

HdM: Matashi mai yin kira a Damagaram

Mahaifin Fauziyya Malam Jibril Kida ya ce tun tasowar ta, tana da hazakar koyon sana'a, abin da ya ce shi ne sirrin nasarorin da ta ke samu. Fauziyya dai ta bayyana cewa ita kam, sun yi hannun riga da aikin gwamnati, tana mai cewa sna'ar da ta ke yi ta wadatar da ita. Masu lura da harkokin yau da kullum na ganin akwai bukar matasa su yi koyi da abin da Fauziyya ta ke yi wajen koyawa 'yan uwansu matasa ayyukan yi domin rage masu zaman kashe wando, wanda hakan galibi ke haifar da ayyukan bata gari tsakanin al’umma.