1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Matashiya mai sana'ar kitso da kunshi

January 5, 2022

Wata matashiya a jihar Sakkwato da ta kammala karatunta har matakin Diploma, ta rungumi sana'ar kitso da kunshi a wani mataki na dogaro da kai da kuma kaucewa rashin aikin yi.

Nigeria Sokoto Haare flechten
Matashiya mai sana'ar kisto da kunshi a SakkwatoHoto: Ma'awiyya Abubakar Sadiq/DW

Matashiyar mai suna Saratu Sulaiman mai Kaset ta ce ta fara kasuwancin ne tun tana aji uku na karamar sakandare a shekarun 2012, kuma karancin masu wannan sana'a ta kitso da kunshi da ta lura akwai na daya daga cikin abubuwan da suka kara jan hakalinta ga wannan sana'a. Matashiyar dai ta bayyana irin yadda sana'ar tata ke kara samun tagomashi da bunkasa, bayan da mutane suka fahimci yadda take gudanar da harkokinta a zamanance.

Koda yake bayan shafe dogon lokaci sannu a hankali kan sana'ar, matashiyar ta ce ta samu rufin asiri sai dai kuma akwai tarin kalubale da take ganin suna mata tarnaki wajen cimma burinta. Baya ga gwamman mutane da matashiyar ta koyawa sana'ar, akwai tarin masu taya ta gudanar da sana'ar a yanzu. Daga karshe dai matshiyar ta ce burinta shi ne koyar da daruruwan matasa sana'ar tata.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani
Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW