1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kaduna HdM: Matashi mai kwale-kwale

February 12, 2020

Wani matashin a jihar Kaduna da ke Najeriya, ya kama sana'ar yasar yashi daga babban kogin Kadunan da kuma daukar mutane da kayayyaki da wani karamin kwale-kwalen da ya hada da kansa.

Afrika Ghana Welt Wasser Tag
Amfani da kwale-kwale domin tsallakar da fasinjoji da kayansuHoto: DW/M. Suuk

Matashin mai suna Halliru Usman dai tun bayan da ya kammala karatunsa a cibiyar horar da malamai ta kasa wato National Teachers Institute Kaduna, ya rufawa kansa asiri ta hanyar kera wani kwale-kwalen katako da yake amfani da shi wajen fiton yashi da daukar fasinjoji da kayayyakinsu dan tsallake babban rafin Kadunan. Halliru ya ce tun bayan kammala karatunsa yake ta fafatukara neman aiki, wannan matsala ce ma ta sanya shi sake tunani wajan samowa kansa wannan sana'ar kuma ya fara ne tun shekara biyar din da suka gabata, abin kuma da ya kawo gagarumin sauyi a rayuwarsa.

Daga cikin nasarorin da ya ce ya samu har da ci gaba da karatunsa da kuma samun karuwar yawan kwale-kwalen da yake kerawa. Yace ya fara ne da kwale-kwale daya kacal, amma ya zuwa wannan lokacin yana da guda biyar. Sai dai duk da ci-gaban da ya samu, ya nunar da cewa akwai kalubale da yake fuskanta wajen gudanar da sana'ar tasa, ciki kuwa har da karancin kudi da kuma tallafi daga hukumomi. Sai dai duk da wannan kalubale, Halliru ya ce koda ya samu aikin gwamnati ba zai karba ba, domin sana'ar kwasar yashi da dakon fasinjoji ta hanyar kwale-kwalen da yake kerwa da kansa ta fi masa aikin gwamnati.