Matashiya mai sana'ar man gyaran fata
March 25, 2020Matashiyar mai suna Sadiya Shehu Adili da akafi sani da Ami Organics ta bayyana cewa ta kammala karatun digirinta ne a bangaren ilimin lissafi a jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto, kuma yanzu haka ta shafe tsawon shekaru uku tana gudanar da wannan sana'ar ta sarrafa 'ya'yan itatuwa zuwa mayuka daban-daban na gyaran fata.
Matashiyar dai ta bayyana cewa lura da yadda ake tsananin fama da cututtukan da ke addabara fata ne a cikin al'umma, ya kara mata kaimi ga karkata hankalinta ga fara wannan sana'a, domin nemawa masu fama da wannan cuta warakar. Ko da yake wannan matashiya ta bayyana cewa akwai tarin kalubale da take fuskanta a sana'ar, sai dai ta ce akwai dimbin nasarori da ta samu sanadin sana'ar.
Matashiyar dai na koyar da 'yan mata 'yan sakandare kan yadda za su gudanar da wannan sana'a. Daga karshe matashiya Sadiya ta ce bata jin za ta iya aje wannan sana'a domin ta rungumi aikin gwamnati, inda kuma tuni ta garagadi takwarorinta matasa da su yunkura su samu sana'a domin kaucewa ganin tasku a rayuwa.