Matashi mai sana'ar gugguru a Kaduna
May 26, 2021Matashi Isa Musa dai, ya inganta sana'ar ta hanyar hada madara da butter da suga kana ya sa sinadarin saka kamshi da sauran kayayyaki. Matashin ya ce tun bayan lokacin da ya kammala daukar horo a kan yadda ake yin sana'ar gugguru, ya fara himmatuwa wajen kama sana'ar domin dogaro da kai. Isa ya kara da cewa, sana'ar na tattare da sauki sannan kuma babu wata wahala da ke tattare a cikinta.
Daga cikin nasarosrin da ya samu dai, akwai yadda wannan sana'ar tasa ke kara samun karbuwa da yadda yake taimakon 'yan uwansa da sauran dangi. Yace na samu damar koyar da matasa masu yawan gaske wannan sana'a, kuma a kullun yana ganin nasara mai yawa da ke cikinta. Duk da irin ci-gaban da ya samu, akwai manyan kalubalen da ke ci masa tuwo a kwarya musamman rashin tsayayyar wutar lantarki a Naajaeriya da kuma matsalar rashin samun irin masarar da ake yin guggurun da ita.