1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hira da Fahim Dashty ɗan jaridar Afganistan

August 8, 2011

Ga mafi yawan al'umar Afganistan ranar tara ga watan Satumbar 2001 rana ce mai tarin muhimmanci kamar yadda ranar 11 ga watan Satumbar shekarar 2001 take ga alumar Amirka.

Hoto: DW/M.Gerner
A ranar tara ga watan Satumba kwana biyu kafin aukuwar hare haren ranar 11 ga wannan wata akan Amirka ne 'yan al-Ƙa'ida suka ƙaddamar da hare hare a ƙasar ta Afganistan waɗanda a cikinsu shugaban gwagwarmayar neman sauyi a ƙasar, Ahmad Shah Massud ya rasa ransa. Fahim Dashty wanda ɗan jarida ne na ɗaya daga cikin waɗanda hare haren na ranar tara ga watan Satumba suka shafa.

"Ina zaune kusa da waɗanda suka ɗaure bama baman a jikinsu."

Fahim Dashty kenan wanda ya kasance a garin Talokan na arewacin Afganistan a ranar tara ga watan Satumbar 2001 kwana biyu kafin aukuwar hare haren 11 ga watan Satumbar 2001 akan Amirka. Fahim ya kasance a tsugune tare da wasu 'yan jarida biyu waɗanda daga bisani suka bayyanar da kansu a matsayin 'yan ta'adda da suka ɓad da kamanninsu.

"Ina zaune ne bayan 'yan bindigar a lokacin da bama bamai suka tashi zuwa can gaba."

Ranar da rayuwa ta canza a watan Satumba

Hoto: DW/M.Gerner

'Yan ta'addar da suka sulalo daga ƙungiyar al-Ƙa'ida sun yi amfani ne da kyamera suka tayar da bama baman da suka ɗaure jikinsu. Nan take wasu dake wannan wuri suka mutu cikinsu har da Ahmad Shah Massud da ake wa kallon gwarzo a yaƙin da ake yi da Taliban da kuma boren adawa da mamayar da Tarayyar Sobiet ta yi wa ƙasar ta Afganistan.

Dashty dai ya tsira da ransa amma ya samu rauni har sai da aka yi masa tiyata a cikin gaggawa. Sai da kuma ya shafe kusan watanni 12 yana juyayin mutuwar Ahmad Shah Massud dake zaman gwarzo a gareshi.

"Ba daɗi mutum yayi magana game da wannan al'amari. A wannan rana mun yi asarar dukan abin da muka mallaka."

Dashty da Massud sun fito ne daga garin Panjshir Tal da yayi suna a matsayin cibiyar boren nuna adawa da mamayar da Tarayyar Sobiet ta yi wa Afganistan a shekarun 1980.

Dashty ya so shiga yaƙin a lokacin da yake karatu. To amma sai aka tura shi zuwa birnin Kabul domin ya ci gaba da karatu har sai ya gama. Saboda cewa a wannan lokaci ba shi da ƙarfin shiga yaƙi. To amma bayan da ya gama karatu yayi wa Ahmed Massud aiki a matsayin mai ba da rahoto a filin daga.

"Na sha gane wa idanuna yaƙi da tashin bam bamai da kuma mutane da suka rasa rayukansu da waɗanda suka samu raunuka. A wannan lokaci ina ɗan ƙarami. Saboda haka aikina ya tsaya ne kan ba da rahoton abin dake faruwa."

Mawuyacin hali game da 'yancin 'yan jarida

Hoto: DW/M.Gerner

Domin ma nuna adawa ne ya sa aka kafa jaridar mako ta Kabul Weekly a matsayin kafar yaɗa manufar jam'iyyar Shah Massud a lokacin mulkin Taliban. Daga bisani dai Dashty ya samu damar kama aikinsa bayan da aka sake buɗe wannan jarida a shekarar 2002. Yanzu yana aiki ne a matsayin babban edita da ke da ma'aikata 12 a ƙarƙashinsa. Dashty ya kan soki gwamnatin Karzai bisa kauce wa tafarkin demukraɗiyya a duk lokacin da ya samu damar yin hakan.

"Wata rana wani babban jami'i na gwamnati yayi mani hannunka mai sanda da cewa mai yiwuwa ne in samu haɗarin mota. Ya ce akwai wata maƙarƙashiya da ake ƙullawa domin yi mini kisa. Ban dai nuna damuwa da jin wannan labari ba. Amma kuma na fahimci wannan saƙo."

Bayan haka ne aka gudanar da zaɓen shekarar 2009 da aka yi zargin tafka maguɗi a cikinsa inda jaridar Kabul Weekly ta buga rahoto da a cikinsa ta soki gwamnati da yin murɗiya a wurare daban daban, abin da ya janyo wa Dashty baƙin jini gun abokan cinikinsa.

"An samu wasu kamfanoni da suka mara wa Karzai baya a yaƙinsa na neman zaɓe waɗanda saboda sukan da na yi masa suka janye sanarwar da suke yi ta jaridarmu, abin da ya janyo mana asarar kuɗi mai yawa.

A dai watan Maris na wannan shekara ne Dashty ya yi ƙoƙarin ta da komaɗar jaridar tasa bayan da ta yi ƙasa a gwiwa. Kuma ko da yake yana fuskantar barazana daga tsarin kasuwanci a yankin Hindukush, amma zai iya cin gajiyar aikin da dakarun yamma ke yi a ƙasarsa Afganistan.

Mawallafa: Martin Gerner / Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal