1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaLebanon

Hizbulllah ta gargadi Isra'ila a kan harin da za ta kai mata

Abdoulrazak Garba Babani
August 1, 2024

Jagoran Hizbulllah na Libanon Hassan Nasrallah, ya gargadi Israila da cewar ta jira martini mai zafi kana maras kyau daga kungiyar bayan kashe babban kwamnada soji na kungiyar Fuad Chokr.

Hoto: Hussein Malla/dpa/picture alliance

 Hassan Nasrallah wanda ya bayyana haka a cikin  wani jawabi da ya yi ta gidan talbijan a sa'Ailin jana'izar  Chokr. Ya ce Isra'ila, ba ta san ba, ta taka jan layi a kan kisan da ta aikata a baya-bayan na shugaban Hamas Ismail Hanieye da ma sauran mayaka na Hizbullah daHamas.