Shugaba Hollande zai je Afirka ta Tsakiya
May 6, 2016Talla
Wannan rikici dai ya kusa rikidewa izuwa yakin basasa. Rahotanni sun nunar da cewa Hollande zai kai ziyarar ne a ranar 13 ga wannan wata na Mayu da muke ciki, a wani yunkuri na yin alkawarin da ma nuna samun goyon bayan Faransa a shirin zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar domin kawo karshen rikicin da kasar ta yi fama da shi. Kana ana sa ran Hollande zai zarce Tarayyar Najeriya a ranar 14 ga watan na Mayu domin halartar taron yankin Afirka ta Yamma da zai mayar da hankali kan yaki da kungiyar ta'addan Boko Haram da ta addabi Najeriya da wasu makwabtanta.