Hong Kong: Hari kan masu zanga-zanga
July 21, 2019Talla
Kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP ya ruwaito cewa ko a gundumar Yuen Long dab da iyakar yankin da kasar China a arewa maso gabashin Hong Kong, wasu mautane da suka rufe fukokinsu sun kai hari ga masu zanga-zanga, tare da jikkata wani dan jaridar mai aikewa jaridar Stand News labarai.
A yau din nan ne dai wata sabuwar zanga-zanga ta sake barkewa a yankin na Hong Kong, a ci gaba da nuna adawa kan wani kudurin dokar hukunta masu laifin yankin a kasar China.