Kalubalen masu zanga-zangar Hong Kong
November 19, 2019Talla
Jami'an tsaron dai sun shiga rana ta uku da kewaye jami'ar yankin Hong Kong din. rahotanni sun nunar da cewa 600 daga cikin masu zanga-zangar sun fice cikin lumana, inda wasu da dama suka yi watsi da gargadin mahukuntan tare da ci gaba da kasancewa a harabar jami'ar.
Mazauna yankin dai sun bayyana fargaba game da makomar masu zanga-zangar da suke ja da hukuma daga cikin jami'ar, ko da yake jagorar yankin Carrie Lam ta shaidawa manema labarai cewa gwamnati za ta yi kokarin ganin sauran masu zanga-zangar sun fice cikin lumana.