1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hong Kong: Ruwan sama mafi karfi cikin shekaru 140

September 8, 2023

Hukumomi a Hong Kong sun yi gargadin saukar ruwan sama mai karfi da kuma iska bayan da mamakon ruwan sama ya haifar da ambaliyar ruwar a fadin birnin.

Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye hanyoyin birnin Hong Kong na kasar China
Hoto: TYRONE SIU/REUTERS

Gargadin na kasancewa na farko tun bayan wanda aka yi a watan Octobar shekarar 2021. Birnin na kasar China ya fuskanci saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya da ba a taba gani ba cikin shekaru 140.

Masana na cewa, mahaukaciyar guguwar nan ta Haikui ta haifar da saukar ruwan sama mai karfi a lardin Guangdong da ke iyaka da birnin na Hong Kong.

Karin bayani:  Guguwar Haikui na barazana a Taiwan

A yanzu haka dai, gwamnati ta sanar da rufe makarantu sakamakon barnar da ambaliyar ruwan ta haifar, kana aka shawarci ma'aikata da su zauna a gida.

Shugaban birnin na Hong Kong, John Lee ya nuna alhininsa game da iftila'in ya na mai bada umurni ga dukannin masu ruwa da tsaki da su dauki matakin gaggawa.

Ko a makon da ya gabata, Kudancin kasar ta China ya fuskanci mahaukaciyar guguwar nan ta Saola.