1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakon masu zanga-zanga a Hong Kong

Abdoulaye Mamane Amadou
May 27, 2020

Zanga-zanga ta barke a yankin Hong Kong a gabanin mahawarar da majalisar dokoki ke shirin yi don tabbatar da dokar hukunta wadanda suka tozarta take kasar China

Hongkong | Proteste Gesetz Nationalhymne Polizei Festnahme
Hoto: Reuters/T. Siu

Wasu tarin 'yan sandan kwantar da tarzoma a cikin shirin ko takwana sun harba hayaki mai sa kwalla kan masu zanga-zanga a harabar majalisar dokokin yankin Hong Kong, a wani yukuri na dakile zanga-zangar da ka da ta barke gabanin wata muhawarar da majalisar ke shirin yi a yau kan wannan sabon kudrin dokar. Shedun gani da ido sun ce an jibge dubban 'yan sandar kwantar da tarzoma inda suka ja daga a dab da harabar majalisar, a daidai lokacin da ake sa ran tabka muhawarar tare da jefa kuri'ar na'am kan wani  sabon kudrin dokar a game da sha'anin tabbatar da tsaro.