NIjar: Koyon sana'o'i ne makomar matasa?
October 8, 2025
Gwamnatin mulkin sojan ta Jamhuriyar Nijar din, ta kaddamar da wani shiri ne na horas da matasa maza da mata sama da 1000 ayyukan hannu da suka hadar da sake-sake da kere-kere da sarrafa kayan noma da na kiwo.
Shawo kan matsalar rashin aikin yi
Makasudin shirin wanda ke gudana a karkashin sashe na uku na manufofin shugaban mulkin sojan kasar Janar Abdourahmane Tiani shi ne, taimaka wa wajen shawo kan matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa da ta zama ruwan dare.
A babban dakin taro na Academie des Arts Mar tiaux na birnin Yamai gwamnatin mulkin sojan ta tara matasan maza da mata daga yankuna takwas na kasar, inda matasan suka bayyana gamsuwarsu dangane da irin ci-gaban da suka samu sakamakon karin horon a kan yadda za su inganta sana'o'in nasu ko zamanantar da su.
Gwamnati za ta bibiya
Gwamnatin ta sha alwashin shirya bikin baje-kolin kayayyakin da matasan suka samar a lokacin wannan horo, domin ba su damar sayar da su da samun jarin da zai ba su damar kafuwar sana'o'in nasu dan dogaro da kai.