HRW ta ce ana sa yara aikin soja a Somaliya
February 22, 2012Wannan rahoton na human Rights Watch mai shafi 104 , ya na bayyani ne dalla dalla game da hanyoyin da ake bi domin tilasta wa yara ƙanana shiga aikin soje a Somaliya a cikin shekaru biyu na baya-bayannan. ƙungiyar da ta himmatu wajen kare hakkin bil Adama a ko ina cikin duniya, ta dogara ne kan wasu hirarraki 164 da ta yi da yaran na somaliya, ciki kuwa har da 21 da suka yi nasarar tserewa daga hannun 'yan Al-Shabab wajen kafa hujjojinta.
HRW ta nunar da cewa tun bayan rintsaɓewar yaƙin Somaliya tsakanin sahekara ta 2010 zuwa ta 2011, ƙungiyar Al-Shabab ta tilasta ma yara ƙanana, ciki har da waɗanda suke da Ƙasa da shekaru 10 da haihuwa, ɗaukan makamai domin shuga fagen yaƙi da suke yi da gwamnati. Hasali ma dai, wasu daga cikin yaran na somaliya ne ke ƙaddamar da hari ne na ƙunar bakin wake. ƙungiyar ta kuma nunar da cewa Al-Shabab na sace yaran mata da nufin tilasta musu yin wasu aikace aikace na gida, tare da ɗaura musu auren dole da wasu daga cikin 'yayan ƙungiyar. kana ta na barazanar ɗaukan tsauraran matakai da ke kai wa ga kisa akan duk wacce ta kuskura arcewa.
A cewar Tirana Hassane, jami'ar Human Rights Watch da ke kula da bincike game da batutuwa masu sarƙaƙiya, wannan tauyen hakkin yara, zai daƙushe makomar ƙasar ta somaliya baki ɗaya.
"Yaran sune manyan gobe na Somaliya. Amma kuma ba wasu matakai da ake ɗauka domin kare su. Ma'ana a kuɓutar da su daga ayyukan soje da makamantansu. Rashin sauke wannan nauyi, ba a kansu kawai zai iya tasiri ba, amma ya na barazanar ne ga makomar ƙasar baki ɗaya."
Ita dai ƙungiyar ta HRW ta ce dakarun gwamnati riƙon ƙwaryar Somaliya ma ba a barsu a baya ba, wajen tursasa wa yara ƙanana a ƙasar. Hasali ma dai ƙungiyoyin sa kai da suke mara wa gwamnati baya suna sanya yara a sahun gaba a filin daga.Ma'ana suna zame musu garkuwa a fagen yaƙi. Saboda haka ne Tirana Hassana , jami'ar HRW, ta ce yara ba su da galihu ko kaɗan a Samaliya,
"Somaliya, ɗaya daga cikin ƙasashe ne na duniya da ba a kiyaye hakkin yara. A fannin ilimi ga misali, ta na ɗaya daga cikin wuraren da ake samun ƙarancin yara da suka iya karatu da rubutu. kana yara na cikin barazanar a ko wani lokaci. Idan sun sami zarafin zuwa makarata, su na tattare da tababa. A takaice dai, ga yaro abu ne mai wahalan gaske samun ilimi, ko kuma samun rayuwar da ta dace."
Ita dai ƙungiyar Human Rights Watch ta yi kira ga ɓangarorin da ke da hannu a rikicin Somaliya, da su yi wa Allah da ma'aiki, su daina tursasa wa yara ƙanana. Kana ta bukaci ƙasashen duniya da su ɗauki matakan da suka wajaba domin raba yaran Somaliya da cin zarafi da kuma baƙar azaba da gwamnati da kuma al-Shabab ke gana musu a fagen yaƙi da ya yi kaca-kaca da Somaliya.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu