HRW ta fitar dav rahoto kan take hakin dan Adam
January 18, 2018Mista Roth ya ce ko da hotunan bidiyo da tashar talbijin ta CNN ta nuna kan cinikin 'yan gudun hijira 'yan Afirka da ake yi a matsayin bayi a kasar ta Libiya bai basu mamaki ba domin kuwa batu ne da tun da jimawa suka yi ta tsokaci a kai ba tare da manyan kasashe sun ce kala ba. Shugaban na kungiyar HRW ya ce lamarin kare hakin bil-Adama a wannan lokaci na gamuwa da babban sakaci na manyan kasashen duniya:
"Idan ku ka kalli tafiyar wannan duniya, za ku ce wai ina manyan kasashen da aka sani da kokawar kare hakin bil-Adama? Amirka dai ta bace, domin Shugabanta Donald Trump ba mai kare hakin dan Adam ne ba, Britaniya ta mayar da hankalinta kan batun ficewarta daga Tarayyar Turai, Jamus ta dukufa wajen girka sabuwar gwamnati, babban nauyin ya rataya ne kan shugaban Faransa, wanda shi ma idan ka dubi yadda siyasarsa ta kasashen waje ta ke kawai gamo nan kawo can ne."
Kenneth Roth ya yi wadannan kalamai ne albarkacin bikin wallafa rahoton kungiyar ta HRW na 2018 kan cin zarafin bil Adama a duniya.