1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar tunkarar COVID-19 a Najeriya

March 25, 2020

Kungiyar Human Rights Watch mai fafutukar kare hakkin dan Adama, ta zargi gwamnatin Tarayyar Najeriya da rashin samar da isassun likitoci da ma wuraren gwajin annobar COVID-19.

Mikroskopische Darstellung der Coronavirus-Krankheit 2019
Hoto: picture-alliance/Newscom/UPI Photo/CDC

Duk da cewar dai alamun karuwar cutar na kara fitowa fili, sai dai matsalar na kara fito da halin taskun da harkokin lafiya a Tarayyar Najeriya ya kwashe tsawon lokaci a ciki fili. Cibiyoyin gwajin cutar dai har ya zuwa yanzu na zaman guda biyar a kasar da ke da yawan al'umma miliyan 200, sannan kuma alamun yaduwar cutar ke kara bayyana.

Babu isassun kudi da kayan aiki

Human Rights Watch din dai ta ce babu isassun likitoci domin tunkarar cutar sannan kuma babu isassun kudi da ake da bukata domin tunkarar annobar, abun kuma da a fadar kungiyar ya sa ya zama wajibi ga Abuja ta mike a tsaye da nufin hana kai wa ga shiga hali na ha'ula'i da sunan annobar ta Coronavirus. Anniete Ewang ita ce mai bincike ta kungiyar HRW din a Najeriyar, ta kuma ce:

Asibitocin Najereiya na fama da cunkoso da karancin kayan aikiHoto: picture-alliance/dpa

"Abin da muke kokarin nunawa shi ne tsarin lafiya na fuskantar matsaloli, saboda rashin isassun kudi da kayan aikin da ake da bukata. A cikin makon jiya likitoci suka shiga  yajin aiki a Abuja sannan kuma mun san ba a biyan ma'aikatan lafiya kamar yadda ya dace, suna fuskantar karancin abubuwan da suke da bukata domin aikin nasu. Muna kira  da a fara mayar da hankali ga gazawar tsarin na lafiya da ke iya hana su mai da martani kan bazuwar cutar yadda ya dace. Muna kiran gwamnatin da ta farga kafin karuwar bazuwar cutar zuwa yanayin da kowa bai shirya masa ba."

Karuwar masu dauke da COVID-19

Ya zuwa yanzu dai yawan masu dauke da cutar ya kai sama da 45 duk da labari mai dadin da ke fadin wasu a cikin shugabanni na kasar da suka hada da shugaban kasar da mataimakinsa da suka cudanya da babban jami'in mulki na fadar gwamnatin kasar sun tsira. 

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da mataimakinsa Yemi Osinbajo ba sa dauke da CorornavirusHoto: Noso Isioro

A cikin makon da ya gabata dai an gudanar da taron majalisar zartarwar kasar da ma taron majalisar tattali na arzikin da ya kalli halarta ta shugabanni na siyasa a kasar kama daga gwamnoni zuwa ministoci a Abujar. Kuma akalla biyu cikin mahalarta tarukan guda biyu sun kamu da wannan cuta. To sai dai kuma a fadar Dr Ibrahim da ke zaman darakta a ma'aikatar lafiya a Tarayyar Najeriyar al'amura na sauyawa game da yanayin da kasar take ciki ga batun kayan aikin dama ma'aikata.

Sannu a hankali dai kokarin killace kan al'ummar Najeriyar na dada tasiri ama'aikatu da hukumomi na gwamnatin da ke kulle a yanzu, a yayin kuma da mahukuntan birnin Abuja ke amfani da 'yan sanda domin korar al'ummar birnin daga wurare na shakatawar gado.