1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A hukumance wa'adin mulkin Bazoum ya kare

Abdoulaye Mamane Amadou Zainab Abubakar -SB
April 2, 2026

A Jamhuriyar Nijar yau ne wa'adin hambararran shugaban kasa bazoum Mohamed ke cika idan da har yanzu yana kan karagar mulkin kasar Jamhuriyar Nijar

Niger Niamey 2021 I Mohamed Bazoum da Hadiza Ben Mabrouk
Niger Niamey 2021 I Mohamed Bazoum da Hadiza Ben MabroukHoto: Boureima Hama/AFP

A ranar biyu ga watan Afrilu na 2021, Mohamed Bazoum ya karbi ragamar kama mulki a Nijar a yayin wani kasaitaccen biki da ya hada fitattun 'yan siyasa da shugabannin kasashe da hukumomi na kasa da kasa, a wannan rana, Nijar bude wani sabon babin da ba ta taba yi ba, domin wani shugaban kasa ya mika mulki ga wani zababben shugaban kasa farar hula.

Sojoji sun sake bayyana a Nijar shekaru biyu da rabi bayan nadin Bazoum

A ranar 26 ga watan Yuli, rundunar sojin Nijar karkashin jagorancin Janar Abdourahmane Tiani sun kifar da gwamnatin Bazoum, sun sanar da rusa kundin tsarin mulki, sun rusa majalisar dokoki da gwamnatin farar hula, bisa wasu hujjojin da suka bayar da tabarbarewar tsaro a Nijar sakamakon hare-haren ta'addanci.

Sojojin da suka kifar da Bazoum sun fuskanci suka da matsin lamba daga waje, ECOWAS ta yi barazanar daukar makai idan ba su dawo da mulkin farar hular da suka hambarar ba, kungiyar tarayya Turai da Majalisar Dinkin Duniya sun yi Allah-wadai da matakin sojin, sun kuma kakaba wa Nijar da sojojin da suka yi juyin mulkin takunkumi, amma kuma tun daga lokacin sojin ke ci gaba da tsare hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum a fadar shugaban kasa.

Niger Niamey | Abdourahamane Tiani shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Hoto: Télé Sahel/AFP

Wa'adin Mohamed Bazoum na shekaru biyar ya cika a ranar biyu ga watan Afirlu 

Idan da sojojin Nijar ba su yi wa Mohamed Bazoum juyin mulki ba e a wannan rana ce ta biyu ga watan Afrilu ne wa'adin mulkinsa ke cika, to amma sai dai ga wasu masu bibiyar siyasar Nijar irin su Soumaila Amadou irin kamun ludayin da Bazoum ya fara da shi ya sha bam-bam da manufar jam'iyyarsa ta PNDS-Tarayya wacce ta kawo shi kan mulki yana cewa : Ba'a je ko ina ba ya fara takon saka da 'yan jam'iyyarsa, ko da ba a yi masa juyin mulki ba da zai fuskanci babban kalubale a cikin gida."

Tambayoyi game da tsare shugaban kasa na dogon lokaci

Ta fuskar doka kuwa yanayin da hambararren shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum yake ciki ba ya da tabbas, domin kundin tsarin mulkin Nijar na shekarar 2010 ya fayyace tsawon wa’adin mulkin shugaban kasa, inda ya kayyade cewar shugaban kasa na wa'adin shekaru biyar har sau biyu.

Dokar ta kuma fayyace cewar idan har ya yi murabus ba ko gaza tafiyar da mulki, shugaban majalisatr dokoki ne ke tafiyar da harkokin mulki a hukumance, kafin yin zaben cike wa'adi a tsawon kwanaki 90, to amma ya wa'adin Bazoum yake a yanzu saboda yaki murabus?

Mohamed Bazoum I Hambararren shugaban kasar Nijar Hoto: Evelyn Hockstein/Pool/File Photo/REUTERS

Dakta Atto Namaiwa, ya ce a duk lokacin da aka karbi mulki da karfin bindiga shugaban kasa ba dole ba ne sai ya yi murabus saboda an karbi mulkin ne da karfi, don haka ranar biyu ga watan Afrilu ba za ta kasance mai muhimanci a fannin shari'a ba. 

Makomar Bazoum a yanzu bayan wa'adin mulkinsa ya kare

Abun jira a gani shi ne matakin da su hukumomin na mulkin soja za su dauka dangane da hambararran shugaban kasar, wanda da dama ke ganin cewa ya danganta da dabi'ar shi Bazoum din, ta rungumar kaddara ko kuma ci gaba da hawa dokin naki wanda hakan ke bai wa wasu damar ja'in ja da hukumomin kasar ta Nijar da suka yi juyin mulkin.

Gaskiyar Magana: Shekara da juyin mulkin Jamhuriyar Nijar

30:32

This browser does not support the video element.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani