1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar CAF ta sanar da lokutan gasar AFCON

May 3, 2026

Hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF ta sanar da cewa gasar cin kofin nahiyar Afirka za ta gudana daga 19 ga Yuni zuwa 17 ga Yuli 2026 a kasashen Yuganda da Kenya da kuma Tanzaniya.

Shugaban hukumar CAF, Patrice Motsepe
Shugaban hukumar CAF, Patrice MotsepeHoto: Wu Tianyu/Xinhua/IMAGO

Hukumar kula da harkokin kwalllon kafa ta nahiyar Afirka wato CAF, ta sanar da cewa gasar cin kofin kasashen Afirka za ta gudana daga ranar 19 ga Yuni zuwa 17 ga Yulin wannan shekara, bayan amincewar da hukumar kwallo ta duniya FIFA ta yi a taron da aka yi a birnin Vancouver na kasar Canada.

Sai dai har yanzu ba a bayyana wace kasar ce a tsakanin Yuganda da Kenya da Tanzaniya, za ta bude gasar da kuma rufe ta ba.

Shugaban hukumar CAF, Patrice Motsepe, ya ce shirye-shirye na tafiya yadda ake bukata, yana mai nuna kwarin gwiwar cewa gasar za ta yi nasara.

Wannan ne dai karon farko da za a shirya wasannin AFCON da kasashe uku tare, haka nan na farko da za a gudanar a yankin gabashin Afirka, tun bayan wacce aka gani a shekarar 1976 a kasar Ethiopia.