Hukumar EFCC ta Najeriya ta ce ta yi nasarori
October 21, 2025
A Najeriya hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa ta EFCC na murna da nasarorin da ta samu a cikin shekaru biyu inda ta kwato kudi Naira bilyan 500 daga hannun wadanda suka aikata cin hanci.
Amma masu rajin yaki da wannan mumunan hali na cewa da sauran babban aiki a gaba, bisa ga dumbin kudaden da aka sace a kasar da zai kai kashi 37 na karfin mizanin tattalin kasar na GDP.
Najeriyar na daya daga cikin kasashen da matsalar cin hanci da rashawa ke yi wa mumunar barna ga tattalin arzikinta, inda kiyasi ya nuna cewa sama da dala biliyan 400 duka an sace su ne ta wannan hanya.
To sai dai a cikin shekaru biyu hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriyar zagon kasa ta EFCC ta samu wadannan nasarori da suka hada da samun hukunci a kan masu halin bera dubu bakwai a kotunan Najeriyar, duk da matsaloli na yawan jinkirin shari'a daga shari'o'in.
Tsabar kudi Naira biliyan 500 aka samu kwatowa daga hannun masu halin bera da shari'a ta tabbatar da sun ci amanar da aka ba su a kasar, a yaki da ake yi da cin hanci da rashawa da ya zama daya daga cikin kalubalen da ke fuskantar Najeriyar.
Kama daga zargi na cushe a kasafin kudi da ake yi wa ‘yan majalisar ya zuwa harkar ba da kwangoli da ko dai ake kara kudade ko a ki yin aiki gaba daya da rahoton gwamnatin Najeriya ya kiyasta cewa an sace dala miliyan 117 ya zuwa jami'an da kan fitar da ta ido, su yi amfani da biro wajen tafka sata, matsaloli ne na cin hanci a Najeriyar da a shekarun baya sai dai a ji shiru.
Ko da yake hukumar mai yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriyar na ta murna na samun wannan nasara a yanzu, ga Comrade Isa Tijjani mai fafutuka a Najeriyar na ganin da sauran aiki.
Duk da cewa gwamnatin Najeriyar ta samar da rijista ta adana dukkanin kudade da kadarorin da aka kwato, amma har yanzu akwai matsala ta sake sace kudaden da aka kwato a yanayin sata ta saci sata.
Kwararru na bayyana bukatar daukar matakin hukunci mai tsauri da dabaru gyara halayen al'ummar kasar don kauce wa ba da cin hanci, domin rahoton da ofishin binciken kudade na Najeriyar ya gano al'ummar kasar sun ba da cin hanci da ya kai sama da dala biliyan daya a tsakanin 2022 zuwa 2023, abin da ya nuna munin wannan matsala da ke neman a yi mata tarba-tarba don rigakafin hana afkuwar ta.