An kada kuri'ar amincewa da sabuwar hukumar EU
November 27, 2019Shugabar Hukumar Kungiyar Tarayyar Turai mai jiran gado, Ursula von der Leyen ta fada a wannan Laraba cewa yaki da sauyin yanayi na zama babban kalubale saboda haka za ta tabbatar da an ware kudade da za su taimaka wajen rage amfani da makamashi irinsu kwal da mai da kuma rage fid da hayaki mai gurbata yanayi.
Von der Leyen ta fada wa majalisar dokokin Turai da ke birnin Strasbourg na kasar Faransa, gabanin kada kuri'ar karshe ta tabbatar da ita a matsayin shugabar hukumar EU cewa ba bu sauran lokaci da za a bata wajen yaki da sauyin yanayi ba.
"Idan akwai wani fannin guda daya da duniya ke matukar bukatar shugabancinmu to shi ne na kare muhalli. Wannan muhimmin batu ne ga Turai da duniya baki daya."
Yanzu haka dai 'yan majalisar Turai sun kada kuri'ar share wa von der Leyen hanyar kama aiki a matsayin sabuwar shugabar Hukumar EU a ranar daya ga watan Disamba, inda wakilai 461 suka ba ta goyon baya yayin da 157 suka nuna rashin amincewa sannan 89 suka yi rowar kuri'unsu.