1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar IAEA ta ce akwai yiwuwar ci gaba da ayyukansu a Iran

Binta Aliyu Zurmi
July 25, 2025

Babban jami'in Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya IAEA Rafael Grossi ya ce ya gamsu da amincewar Iran na karbar bakuncin ziyarar tawaga daga hukumar a 'yan makonnin da ke tafe.

Österreich Wien 2025 | IAEA-Generaldirektor Rafael Grossi vor Notfallsitzung zu Iran
Hoto: Elisabeth Mandl/REUTERS

Grossi ya ce ziyarar ta tawagar kwararru za ta iya bayar da damar masu saka ido na Majalisar Dinkin Duniya komawa Iran din don ci gaba da gudanar da bincike, watakila a cikin wannan shekarar.

Mista Grossi ya shaidawa manema labarai yayin wata ziyara da ya kai kasar Singapore inda ya ce idan ba su koma da wuri ba, za a iya fuskantar babbar matsala, a cewarsa wannan wani nauyi ne da ya rataya a wuyan Iran.

A farkon watan Yuli ne wata tawagar hukumar ta IAEA ta fice daga Iran yayin wata ziyara da ta kai bayan da Tehran ta sanar da dakatar da huldarsu.

Iran ta zargi hukumar ta IAEA da bakinta a hare-hare da aka kai cibiyoyinta na nukiliya a watan Yuni, wanda Isra'ila ta ce ta kaddamar da su ne domin hana ta kera makamin nukiliya.

A ranar 22 ga watan Yuni ne Amurka ta kai nata hare-hare a kan cibiyoyin nukiliyar Iran da ke Fordo da Isfahan da kuma Natanz.

Karin Bayani: Iran da wasu kasashen Turai na shirin zama a Turkiyya kan shirin nukiliyar Teheran