Hukumar IAEA ta kada kuri´ar amincewa da wani kuduri kan Iran
February 4, 2006Hukumar da ke kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA ta kada kuri´ar yin karar Iran a gaban kwamitin sulhu na MDD akan aikace aikacenta na nukiliya. Kasashen 27 daga cikin 35 na hukumar ta IAEA suka jefa kuri´ar amincewa da kudurin, 3 suka nuna adawa da shi yayin da 5 suka yi rowar kuri´unsu. Wannan matakin dai ya biyo bayan shawarwarin da aka shafe kwanaki da dama ana yi ne a hedkwatar hukumar dake birnin Vienna. Hakazalika wannan mataki ka iya share fagen sanyawa Iran takunkuman MDD na karya mata tattalin arziki. Bayan kada kuri´ar shugaban tawagar Iran a hukumar ta IAEA ya fadawa manema labarai cewa kasarsa zata mayar da martani inda zata ci-gaba da shirin samar da sinadarin uranium sannan zata takaita ba wa jami´an hukumar IAEA izinin gudanar da bincike a tashoshinta na nukiliya.